An kama waɗanda ake zargi da sace alamar ofishin ƴansanda a Kano




Rundunar ƴansandan jihar Kano ta kama mutane 2 da ake zargi da sace allon alama na ofishin 'yansanda dake karamar hukumar Ungogo.

Mai magana da yawun rundunar 'yansandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya kara da cewa an kama mutanen da taimakon al'ummar yankin.

"Wanda ya saci 'Bachirawa Police Station (Sign Post)' da wanda ya karba sunzo hannu. Mutanen Unguwar sun kawo sabon "Sign Post",  inji mai magana da yawun 'yansandan.

Ana zargin an sace allon alamar ne a yayin zanga-zanga da ta gudana a makwannin da suka gabata.

Zanga-zangar ta matsin rayuwa ta rikide zuwa rikici a jihar Kano bayan bata gari sun fara lalatawa da sace kadarorin al'umma da na gwamnati.

Post a Comment

Previous Post Next Post