An kama mutane 4 bisa zargin harin caka wuka a kan mahaifin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal

 


An kama wasu mutane hudu bayan harin wuka da aka kai kan mahaifin matashin dan wasan kwallon kafa na kasar Spain da Barcelona, Lamine Yamal a yankin Catalonia, kamar yadda ‘yan sandan yankin suka shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, a yau Alhamis.

An kai harin ne da misalin karfe 7:10 agogon GMT a jiya Laraba a wani wurin ajiye motoci a garin Mataro na Catalonia mai tazarar kilomita 30 daga Barcelona, ​​a unguwar Rocafonda inda Lamine Yamal ya fito, in ji kakakin hukumar Mossos d'Esquadra, 'yan sandan yankin na Catalonia. 

An caka wa mahaifin Yamal, mai suna Mounir Nasraoui wuka sau da yawa a jikinsa, kamar yadda 'yan sanda su ka baiyana, kuma ya na jinya a asibitin Can Ruti, sai dai kamfanin dillancin labarai na AFP ya kasa samun jin ta bakinsa.

Wata majiya da ke kusa da iyalin Yamal ta shaida wa AFP cewa yanzu Nasraoui "ya fita daga cikin hadari" kuma "an ci gaba da sa ido a kansa" amma yana cikin "hayyacin sa".

Da aka tambaye shi game da abubuwan da suka faru da kuma yiwuwar sallamar Yamal  daga asibiti, majiyar ta ƙi yin karin bayani.

An kama mutane uku a daren Laraba kuma ana yi musu tambayoyi a ofishin ’yan sanda na Mataro, yayin da na hudun kuma aka kama shi da misalin karfe 9 agogon GMT na safiyar yau Alhamis.

Post a Comment

Previous Post Next Post