Majalisar Manyan Ƙasa, NCS, da dukkan gwamnoni 36 sun aminta da kamun ludayin mulkin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Majalisra da gwamnonin sun aminta da salon mulkin shugaban kasar ne a ganawar da yayi dasu daban-daban a jiya Talata.
Bayan ganawa da majalisar wacce ta kunshi tsoffin shugabannin Nijeriya da gwamnoni da manyan jami'an gwamnati, shugaban kasar ya sake ganawa da gwamnoni dukka a ranar.
Gwamnan jihar Kwara, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, AbdulRazaq Abdulrahman ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Acewarsa, sun aminta da salon mulkin na shugaban kasar ne bayan ministoci sun yi bayani kan ci gaban da aka samu a ma'aikatunsa ga majalisar magabata ta kasar.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan da Yakubu Gawon da Abdussalam Abubakar ne dai suka halarci taron.
Sai dai ba a ga tsohon shugaban kasa, Olesugun Obasanjo ba.
Tags:
LABARAI