A jiya Laraba ne ƴanbindiga su ka yi garkuwa da wani jami’in ƴansanda na Mopol, a kusa da kauyen Kampani da ke karamar hukumar Wase a jihar Plateau.
Lamarin dai kamar yadda majiya daga yankin ta bayyana, ya faru ne da yammacin jiya Laraba a lokacin da dan sandan da wani soja ke kan hanyarsu ta zuwa yankin Zurak zuwa garin Kamapani, inda ƴan bindigar suka yi musu kwanton-bauna.
Majiyar ta ce yayin da aka sace dan sandan, sojan shi kuma ya samu nasarar tserewa.
Majiyoyi daga yankin sun shaida wa Daily Trust cewa sojan da jami’in ‘yan sandan na aiki ne tare da tawagar jami’an tsaro da ke aikin samar da zaman lafiya a ƙauyukan Bangalala, Kampani, Zurak, da sauran garuruwan da ƴanbiinduga suka addabar.
Sahapi Sambo, shugaban matasan yankin wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, “Dukkan su biyun sun nufi garin Kampani ne wajen abokan aikinsu amma sai aka kai musu hari a kan hanyarsu.
" Al'ummar da ke kewayen yankin na fama da ayyukan 'yan bindiga a wasu lokuta kuma shi ya sa a ko da yaushe jami'an tsaro ke sintiri don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi. Don haka, har ya zuwa yanzu, ba mu ji inda dan sandan ya ke ba.”
Shugaban matasan ya kara da cewa jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda da ’yan banga a ranar Alhamis, sun bi sawun ‘yan bindigar zuwa maboyarsu domin kubutar da dan sandan da aka sace.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, bai amsa tambayar da wakilin Daily Trust ya yi kan lamarin ba.
Tags:
LABARAI