Kamfanin Zhongshan na kasar China ya bayyana sakin jirgi guda daga jiragen fadar shugaban kasar Najeriya guda 3 da ya sa kotu ta kwace masa saboda rikicin kwangilar da ya ke yi da gwamnatin jihar Ogun. Zhongshan ya ce ya amince a saki jirgin guda ne saboda bai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu damar amfani da shi domin zuwa kasar Faransa don ganawa da shugaba Emmanuel Macron. Kamfanin ya ce ya amince da sakin jirgin ne domin nuna aniyarsa ta neman sulhu dangane da matsalar. Zhongshan ya maka gwamnatin Ogun da ta Najeriya a kotun London a shekarar 2018 inda ta bai wa Najeriya umarnin biyansa dala miliyan 70 a matsayin diyya amma hukumomin Najeriya suka ki. Ya zuwa yanzu wannan kudin ya tashi zuwa dala miliyan 81.
📷 Daily Trust