Ko kun san masu shirin jagorantar zanga-zanga a Najeriya?

Wasu ƙungiyoyi da ke shirin jagorantar zanga-zanga a Najeriya, sun fito sun bayyana kansu a wani taro da suka gudanar a jihar Kano a ranar Talata.


Gamayyar ƙungiyoyin daga arewacin Najeriya sun jaddada cewa ba gudu ba ja da baya za su fito zanga-zangar da suka ce za su jagoranta a sassan arewacin kasar, duk da gargaɗi da roƙon gwamnati su ƙara haƙuri su jingine zanga-zangar.

Ƙungiyoyin sun shirya gudanar da zanga-zangar ta kwana 10 daga ranar Alhamis 1 ga Agusta.

Sun ce zanga-zanga ita ce kawai zaɓin da ya rage masu domin nuna fushinsu kan halin da Najeriya ke ciki na matsalolin tattalin arziki da tsaro.

Amma hukumomin gwamnati na ci gaba da gargaÉ—in yiyuwar tashin hankali kuma wasu na iya amfani da zanga-zangar su wawushe dukiyoyin al'umma.

Farashin kayan masarufi a Najeriya sun yitashin gauron zabi da ba a taɓa gani ba a tarihi, ɗaya daga cikin dalilin da ke ingiza zanga-zangar da ta ja hankali a shafukan sada zumunta.

Masu shirin jagorantar zanga-zangar kuma yanzu sun fito sun faɗi dalilansu da kuma buƙatu da yadda suka tsara gudanar da zanga-zangar.


Waɗanne ƙungiyoyi ne?
Wata gamayyar ƙungiyoyi ƙarƙashin inuwar kungiyar tabbatar da kishin kasa ta NPFM ta fito ta bayyana kanta da cewa ita ce za ta jagoranci zanga-zanga a arewacin Najeriya.

Bayan taron da suka gudanar a jihar Kano a ranar Talata, ƙungiyoyi 13 na arewacin Najeriya sun jaddada aniyarsu ta jagorantar zanga-zangar, a cikin wata sanarwa da suka fitar.

Sun ce ba gudu ba ja da baya za su fito zanga-zanga kamar yadda suka tsara gudanarwa daga ranar Alhamis 1 ga Agusta a sassan arewacin Najeriya.

Masu jagorantar zanga-zangar sun bayyana sunayensu tare da gabatar da buƙatu da umarni na matakan da suka ɗauka daga ranar 1 ga watan Agusta da za su soma zanga-zangar.

Sun ce zanga-zangar da za su yi ta lumana ce kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su dama.

Daga cikin bukatun zanga-zangar da suka zayyana sun haɗa da tilasta wa gwamnati rage farashin litar man fetur tsakanin N160 zuwa N200 da rage farashin kayan abinci da lantarki da kudin ruwa da kuma rage kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati tare da kawo ƙarshen matsalolin tsaro a Najeriya.

Sannan masu shirya zanga-zangar sun tsara umarni ga waÉ—anda za su shiga zanga-zangar.

"Babu buƙatar wani ya ɗauki makami, kuma kada wanda ya nemi ya ci zarafin wani ko yunƙurin tayar da hankali," kamar yadda suka bayyana cikin sanarwar da suka fitar

Sannan a cikin umarnin sun haramta wawushe dukiyar mutane.

Kungiyoyin sun kuma fadi lokaci da wuraren da za su hadu domin zanga-zangar.

Post a Comment

Previous Post Next Post