Gwamnan Kano ya nemi tallafin gidauniyar Qatar wajen magance matsalolin da suka shafi al'umma



Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya nemi tallafin gidauniyar tallafi ta kasar Qatar wajen magance kalubalen da ake fuskanta a fannin samar da ruwan sha da ilimi da tallafawa mata.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yau Juma'a.

Sanusi Bature ya ce gwamnan yayi rokon ne a yayin da ya kai ziyara ofishin gidauniyar ta Qatar dake Abuja.

Acewarsa, Gwamnan ya bayyana bukatar hadin gwiwa wajen samar da ruwan sha ta amfani da hasken wutar lantarki.

Gwamnan ya kuma bukaci gidauniyar da ta kara gina rukunin gidaje a filayen da gwamnati za ta bayar domin tallafawa masu karamin karfi.

Anasa jawabin, Daraktan gidauniyar, Elsayed Mohammed Abdou Hamdi ya yabawa gwamnan bisa ziyarar da ya kai domin amfanuwar al'ummar Kano.

Sannan ya tabbatar da cewa gidauniyar zata samar da tallafi ga al'ummar jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post