Gwamnatin Najeriya taki bayyana wuraren sayar da shinkafar dubu 40
dgwamnatin ta bayyana dalilin da yasa ba za ta sanar din ba
HimmaTv ta ruwaito ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema ranar laraba a Abuja.
Idris ya ce wannan shiri na daya daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin Tinubu ta fito da su domin saukakawa yan kasa tsadar rayuwa.
Sai dai da yake magana a ranar Laraba ministan ya ce ana shirin raba buhunhunan shinkafar zuwa jihohin Nigeria.
Ya kara da cewa, ba za a iya bayyana wuraren da za a sayar da su a fadin kasar nan ba saboda dalilai na tsaro, kuma don tabbatar da cewa talakawa da akai tsarin don su sun sami shinkafar.
“Zai yj wahala a ambaci wuraren da za a sayar da Shinkafar saboda dalilan tsaro.
“Amma muna da shinkafar a kasa, kuma za a sayar da ita a kan N40,000.