Shugabannin za su gudanar da taron ne a sabon ginin zauren ‘yan majalissun dokokin Zimbabwe, wanda kasar Sin ta tallafa wajen ginawa, wanda kuma ke kan shahararren tsaunin nan na Hampden, mai nisan kilomita 18 daga birnin Harare.
Harabar ginin dai na da fadin sakawaya mita 33,000, yana kuma da manyan sassa 2, sassan ofisoshi mai hawa 6, da ginin zaurukan ‘yan majalissa mai hawa 4.
A watan Oktoban bara ne gwamnatin kasar Sin ta mika sabon ginin ga gwamnatin Zimbabwe a hukumance. Kuma taron shekara shekara na kungiyar SADC da za a bude a yau, shi ne babban taro na farko da gwamnatin kasar za ta karbi bakunci a sabon ginin. (Saminu Alhassan)
Tags:
LABARAI