Haka nan, majalisar ta nuna rashin amincewarta ga duk wani yunƙuri na sauyin gwamnati ba ta hanyar zabe ba a zaman da ta yi na yammacin Talata.
Majalisar kan yi zama ne a duk lokacin da wani muhimmin abu ya tunkaro ƙasar, domin bayar da shawarar yadda za a tunkare shi, kuma wannan ne karon farko da Shugaba Tinubu ke jagorantar taron tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.
Majalisar ta ƙunshi tsofaffin shugabannin ƙasar zaɓaɓɓu da na mulkin soja, da gwamnoni, da ministoci, da shugabannin majalisar tarayya, inda suke tattauna halin da ƙasa ke ciki da kuma matakan da suka kamata a ɗauka.
Cikin tsofaffin shugabannin da suka halarci zaman na Talata akwai Muhammadu Buhari, da Goodluck Jonathan, da Abdulsalami Abubakar, da Yakubu Gowon, wanda ya halarta ta bidiyo.
Ƙudirorin da majalisar ta cimma
A cewar Ministan Tama da Ƙarafa Dele Alake, gabanin jaddada amincewar majalisar ta saurari bahasi daga ministoci da wasu shugabannin hukumomi kan halin da ƙasar ke ciki a ɓangaren tsaro, da tattalin arziki, da aikin gona, da dai sauransu.
Shugaban Æ™ungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulrahman AbdulRazaq na jihar Kwara, ya ce sau biyu suna kaÉ—a Æ™uri’ar amincewa da shugabancin Tinubu a taron.
“Ina mai farin cikin shaida muku cewa mu ma gwamnoni, kamar Majalisar Magabata, mun kaÉ—a Æ™uri’ar jaddada amincewa da salon mulkin shugaban Æ™asa,” in ji shi.
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe na ciki gwamnonin da suka halarci zaman kuma ya faÉ—a wa wakilin BBC Haruna Tangaza muhimman abubuwan da suka tattauna a zaman:
Tsaro
Gwamnan ya ce majalisar ta tattauna kan matsalolin da suka shafi tsaro a faɗin ƙasar.
“Malam Nuhu Ribadu mai bai wa shugaban Æ™asa shawara kan tsaro ya ba mu cikakken bayani kan halin da ake ciki da kuma matakan da ake É—auka a yanzu,” in ji gwamnan.
Tattalin arziki
Ministoci sun gabatar da bayanai da suka shafi tattalin arziki.
“Ministan kuÉ—i ya kawo bayani kan yanayin tattalin arziki.”
Yunwa
“Haka nan, shi ma ministan noma ya yi bayanai kan halin da ake ciki game da tsadar farashin kayan abinci a faÉ—in Æ™asa, inda aka faÉ—a yanayi kamar na yunwa.”
Da aka tambaye shi ko akwai wasu ƙudirori takamaimai da suka cimma bayan jin waɗannan bayanai, sai ya ba da amsa da cewa:
“Ba Æ™udirori ba ne kawai, sun ba mu bayanai ne da kowa zai je ya duba, sannan kuma gwamnati ta É—auki matakai a gwamnatance.”
Abin da shugaban ƙasa ya faɗa wa gwamnoni
Bayan kammala taron majalisar Shugaba Tinubu ya sake keɓewa da gwamnonin jiha, inda suka sake yin wata ganawar.
“Abubuwa ne da suka shafi dangantakar gwamnoni da gwamnatin tarayya, musamman saboda matsalar da aka samu yayin wannan zanga-zanga, da kuma buÆ™atar mu haÉ—a kai,” a cewar Gwamna Inuwa Yahaya.
“Ma’ana ya kasance gwamnatocin jiha da na tarayya suna tafiya kan babi É—aya ba tare da an samu bambance-bambance ba, saboda bambanci zai iya kawo mana damuwa.”