Ƙungiyar kare hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta yi kira ga Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta kafa kwamitin bincike domin bincikar kisan da aka yiwa masu zanga-zanga a yankin Kurna da Kofar Nasarawa.
A wata sanarwa da ta aikawa jaridar Daily Nigerian, Amnesty International ta ce "dole ne a binciki yadda jami'an tsaro suka gudanar da ayyukansu da ayyukan ɓata gari da aka yo haya suka lalata dukiyoyi.
" Kwamitin binciken dole ne ya yi aikinsa a bayyane kuma a samar masa da dukkan abinda yake bukata wajen gudanar da aikin nasa. Hakan ya hada da kudaden gudanar da aiki da samar da kwararru wajen bincike da masana shari'a."
Ƙungiyar ta kara da cewa gaza yin binciken kan abinda jami'an tsaro da bata gari suka yi zai haifar da koma baya wajen bin doka da oda.