Rundunar ƴansanda a jihar Borno ta tabbatar da kama wasu mutane tara da ake zargi da ɗaga tutocin kasar Russia a yayin zanga-zanga a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Kwamishinan ƴansanda na jihar, Yusuf Lawal ne ya bayyana haka a yau Talata yayin da ya ke bayar da rahoton halin da ake ciki da jihar ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Maiduguri.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a unguwar Zannari Tamsu da ke unguwar Gwange, Maiduguri a ranar 5 ga Agusta, 2024.
Mista Lawal ya ce wadanda aka kama sun hada da Khalafi Abdulhamid, Mohammed Abubakar, Mohamed Ibrahim, da Abba Hassan, dukkansu mazauna yankin Zannari Tamsu ne.
“Sauran waɗanda ake zargin, Bashir Ahmad, Musa Lawan, Abba Mallam, Habibu Auwal, da Inusa Abdullahi, an mika su zuwa Crack Squad domin gudanar da bincike mai zurfi, tare da gurfanar da su a gaban kotu,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce an fara dakile zanga-zangar, inda ya ce ‘yansanda za su ci gaba da sanya ido da kuma sintiri a yankin domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.