Ƙasashen duniya sun buƙaci al'umominsu mazauna Lebanon su fice daga ƙasar

 Ƙasashen duniya da dama ciki har da Amurka, na ci gaba da kiraye-kiraye ga al'umominsu da ke zaune a Lebanon su gaggauta ficewa daga ƙasar, sakamakon ƙaruwar fargabar ɓarkewar yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta sha alwashin mayar wa Isra'ila mummunar martani kan zarginta da kisan shugaban Hamas Ismail Haniyeh a birnin Tehran ranar Laraba.


Har yanzu dai Isra'ila ba ta ce komai ba game da kisan shugaban na Hamas.


Mutuwarsa na zuwa ne sa'o'i bayan harin Isra'ila ya kashe babban kwamandan ƙungiyar Hezbollah Fuad Shukr a birnin Beirut.


Jami'an ƙasashen Yamma na fargabar cewa ƙungiyar Hezbollah a Lebanon da ke samun goyon bayan Iran za ta taka rawa a martanin da Iran ɗin za ta mayar, wanda kuma ka iya haifar mummunar martani daga ɓangaren Isra'ila.


Amurka da wasu ƙasashen Yamma na ci gaba da yunƙurin yayyafa ruwa ga wutar da ke ƙoƙarin tashi a yankin.


Kawo yanzu dai ƙasashen Amurka da Birtaniya da Sweden da Faransa da Canada da Jordan sun umarci al'umominsu da ke zaune a Lebanon su gaggauta ficewa daga ƙasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post