Gwamnatin Somaliya ta kama wasu manyan jami'an tsaron ƙasar a Mogadishu bayan wani harin ƙunar baƙin wake da na bindiga da aka kai wurin shaƙatawar bakin ruwa na Lido ranar Juma'a.
Aƙalla mutum 37 ne suka mutu wasu fiye da 200 suka jikkata, kamar yadda ma'aikatar lafiyar ƙasar ta bayyana.
Firaministan ƙasar, Hamza Abdi Barre ya ce an kama jami'an ne bisa sakacin tsaro da ya faru har aka kai harin.
A ranar Asabar, shugaban ƙasar, Hassan Sheikh Mohamud ya yi ganawar gaggawa da hukumomin tsaron ƙasar domin nazarin harin.
Fitaccen wurin shaƙatawar na Lido na unguwar AbdiAziz a Mogadishu, babban birnin ƙasar.
Kuma ya kasance wuri mai matuƙar tsaro, sannan unguwar da manyan jami'an gwamnati ke zaune.
A baya ƙungiyar Al-Shabaab ta sha yunƙurin kai wa unguwar hare-hare.
Tags:
LABARAI