Wata sanarwar da IAEA ta fitar, ta ce masananta dake tashar, sun ziyarci wurin da harin na jiya ya aukawa wato titin dake kewayen tashar, wanda ke kusa da muhimmiyar matattarar ruwa dake sanyaya tashar, kuma kimanin mita dari daga layin wuta na Dniprovska dake tashar
Ta kara da cewa, duk da cewa ba a samu jikkatar mutane ko lalacewar kayayyaki a tashar ba, harin ya lalata titin dake tsakanin manyan kofofin tashar biyu.
Darakta janar na hukumar Rafael Grossi, ya nanata kira ga dukkan bangarorin da su kai zuciya nesa.
Bugu da kari, hukumar ta ce, masanan dake wurin sun bayar da rahoton karuwar ayyukan soji a yankin cikin makon da ya gabata, ciki har da kusa sosai da tashar, kuma babu alamun tsagaitawar ayyukan sojin.