Mazauna yankin arewacin Najeriya na dandana kudar su sakamakon tsadar farashin man fetur sabanin yadda matsalar take a yankin kudu.

 


 Rahotanni daga sassa daban daban na arewacin kasar na nuna cewar farashin litar man ya tashi ne daga naira 700 zuwa dubu guda. Wasu yankunan sun ce farashin kan haura dubu guda saboda yadda ba'a samun sa a gidajen man NNPC ko kuma na manyan dillalai. Wannan ya saba da yadda ake sayar da litar man a yankin kudu, musamman birnin Lagos, inda kamfanin NNPC ke sayar da lita guda a kan naira 568, yayin da gidan man dillalai masu zaman kan su ke sayar da shi a kan naira 600 zuwa 630. Kungiyar dillalan man ta danganta matsalar da rashin samun man daga hannun kamfanin NNPC, inda take cewa ita ma tana saye ne a hannun wasu dillalan dake shiga da shi cikin  kasar. Wannan matsalar ta haifar da tsadar sufuri da kayan masarufi a sassan arewacin kasar.


📷 NNPC

Post a Comment

Previous Post Next Post