Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta kudu ya ce ba wasu kuɗaɗe ba ne ƴan majalisar ke samu da har zai zama wani abin cecekuce game da albashinsu.
Sanatan na mayar da martani ne kan kalaman tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Sanata Shehu Sani kan albashin sanatocin.
A tattaunawar da yayi da sashin Hausa na BBC, Kawu Sumaila ya ce “Kuɗin da ake karɓa na albashi a wata bai kai Naira miliyan ɗaya ba, idan an yi yanke-yanke yakan dawo kamar naira dubu ɗari shida da ɗan wani abu a matsayin albashi,” in ji sanatan.
Ya ce hukumar hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta Najeriya ce ta yanka wa ƴanmajalisar albashin.
Sai dai Sanata Kawu Sumaila na jam’iyyar hamayya ta NNPP ya ce kudaden gudanarwa da yake samu a matsayinsa na ɗanmajalisar dattawa da ya ƙunshi har da tafiyar da ofis ya kai naira miliyan ashirin ɗaya a kowane wata.
“Saboda ƙari da aka samu, a majalisar dattawa ana ba wa kowane sanata naira miliyan ashirin da ɗaya a kowane wata a matsayin kuɗin gudanar da ofis ɗinsa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jimillar naira miliyan 22 yake yake samu a matsayinsa na sanata.
“Ni dai ban san wani kuɗi da aka halarta ake ba ni a matsayin sanata ba,” a cewarsa.
Ya ce kuɗaɗen da yake karɓa su ne na dukkanin ayyukan da zai yi da suka haɗa da tafiye-tafiye ɗanmajalisa na cikin gida da sayen jaridu .
Sai dai ya ce bai san adadin kuɗin da shugabannin majalisar ke karɓa ba a matsayin albashi da na gudanarwa.
Sanatan ya caccaki Obasanjo inda ya ce a zamanin mulkinsa ne aka fara ba ƴanmajalisa Kudaden da suke wuce hankalin mutane da nufin gyara ga kundin tsarin mulki domin sahalewa Obasanjo yin tazarce, zargin da a baya tsohon shugaban ya musanta.