Daga Aliyu Samba
Ina mamakin yadda yan adawar gwamnatin Tinubu musamman waɗanda ya kayar a zaɓe suke ɓuya bayan masu cewa a dawo da tallafin mai, alhalin dukkan su suna kan ra'ayin cire ci domin shine kaɗai maslahar ƙasar nan, amma fa muddin in ana buƙatar samar da gyara wanda bazai zama na wucin-gadi ba.
Peter Obi na jam'iyyar Labour kafin zaɓe ya bayyana cewa zai cire Tallafin Mai kamar yadda za a ji daga bakin sa a bidiyon dake ƙasa, haka takwarorin sa na ragowar jam'iyyun da suka shiga babban zabe da ya gabata, amma a yanzu Obi na daga masu ingiza wutar tunzura matasa da su fito a yi uwar watsi a ƙasar nan in ba dawo da subsidy ba.
Wani abu da mutane da dama basu sani ba shine, gwamnatin Tinubu ta zabi daukar matakin da zai hana Najeriya taƙaita a iya siyar da ɗanyan mai ne, zata fara tace shi tare da fitar da Man Fetur, Dizal da Gas daga nan cikin gida Najeriya don amfanin mu da kuma fitar da shi waje don haɓaka tattalin arziƙin mu. Wannna zai kara ribanya tattalin arzikin kasar tare da samar da man a farashi mafi sauƙi daga yadda ake siyan sa a baya.
Wannan dalilin ya sanya Gwamnati ta karkatar da triliyoyin Nairori da ake kashewa da sunan tallafin mai, wanda wasu ke sacewa, a ƙaƙabawa Najeriya bashin da baza ta iya biya ba, har hakan ya zama takunkumin da saidai a yi ta bada ɗanyen mai dan cike wancan gurbin da wasu suke sacewa zuwa aikin farfado da matatun man kasar da suka durkushe.
Wani abin da ya kamata a sani, waɗannan masu sacewa da wawushe triliyoyin nairori, sune ke da manyan hannayen jari a kusan duk masana'antu dake samar da ababen buƙatar talaka na yau da kullum, shiyasa suka tsananta farashin su don talaka yayi wa gwamnati bore kan lallai sai ta dawo da tallafi, su kuma su cigaba da cin Karen su ba babbaka, ƙasa ta ci gaba da tsiyacewa.
Wannan matsalar ce Shugaba Tinubu ya dasa wa aya, ya kuma mai da ƙarfi wajen farfado da matatun mai mallakin Najeriya, wanda ana sa ran kammala aikin su nan da shekara mai zuwa.
Tun bayan janye wannan tallafi da ya bayyana a bara, shugaba Tinubu ya riɓanya kuɗaɗen da ake aikawa Gwamnonin jihohi tare da ware biliyoyin Nairori don samar da wasu hanyoyi da zasu kawo sauƙin rayuwa ga al'umma. Hatta kayan noma da takin zamani sai da aka raba zuwa dukkan jihohi don gwamnoni su bada filaye da zasu kai eka milyan 10 a fadin kasar don a noma abinci, wanda wadatar sa zai sa dole a samu sauƙin sa a fadin kasar.
Maimakon yin abinda zai shafi inganta rayuwar talakawa, sai da yawan gwamnonin suka karkatar da kudaden zuwa wasu ayyukan da ba su ƙasa da al'umma ke buƙata ba cikin wannan yanayi ujila. Ganin wannan kalubale, Shugaba Tinubu ya shigar da gwamnonin ƙara zuwa Kotun Koli don hana su ikon tasarrufi da kudaden ƙananan hukumomi da a baya suke dabdala da su.
Gwamnatin tarayya tayi nasara kan gwamnonin inda a yanzu kai tsaye kudaden kananan hukumomi wanda aka ribanya su zasu ke isa kai tsaye ga ciyamomi, wanda aikin da za ayi dasu kacokan shine abinda ya shafi rayuwar al'umma kai tsaye a matakin kowacce karamar hukuma. Wannan ya rage harkar kashe-mu-raba da gwamnonin ke yi a baya da ciyamomi, wanda ya jefa kananan hukumomin cikin mawuyacin hali.
Dukkan mu mun sani, ba yadda zaka ɗaura ƙafar mutumin da ya karye ace ba zai sha azaba ba, amma azabar zata zama ta wucin-gadi ce, sannu sannu zai warke ya kuma tashi kyam akan diga-digan sa. Kwatankwacin haka Najeriya ke ciki a yanzu, ba shakka waɗannan matakan zasu zo da raɗaɗi domin ta taba maslahar wasu mutane dake sace kuɗaɗe a kasar nan, amma kuma waɗannan matakan a yanzu sune maslahar ƙasar mu da al'ummar mu muddin muna son mafita mai ɗorewa ga manyan matsalolin da suka dabaibaye Najeriya.
Mun yi hakuri, mu cigaba da yi, ba za mu ga komai ba sai ribar hakan. Muna da kyawawan fata akan Shugaba Tinubu, mun sani cewa al'umma na cikin mawuyacin yanayi, amma mu sani, wadanda ke amfana daga matsalolin mu ne ke iza wutar wannan raɗaɗin, kuma da yardar Allah baza su kai banten su ba. Najeriya zata farfado, kuma duk taɗiyar da suke yi da zagon ƙasa zai zama tarihi.
#WeBelieveInBat
#RenewedHope