NJC za ta ladabtar da wasu kangararrun alkalai guda 4



Hukumar kula da aikin shari'a a Najeriya ta NJC ta sanar da kafa kwamitoci domin ladabtar da wasu kangararrun alkalai guda 4 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka. NJC ta kuma ce ta sanya wasu alkalan 5 cikin wadanda za ta ci gaba da sanya ido a kan su, ya yin da ta gano wasu 215 da ta ce basa gudanar da ayyukan su yadda ya kamata a fadin kasa baki daya. Sai dai mai magana da yawun hukumar Soji Oye bai gabatar da sunayen wadannan alkalai da za'a ladabtar ba da kuma wadanda aka bayyana cewar ba sa aiki yadda ya kamata. Bangaren shari'a na daya daga cikin hukumomin da 'yan Najeriya suke kuka da shi saboda rashin samun adalci ga mutanen da aka zalunta ko kuma daukar dogon lokaci kafin kammala shari'a. Wani binciken hadin gwuiwa da Cibiyar McArthur ta jagoranta watannin da suka gabata, ya bayyana alkalan a matsayin wadanda suka fi karbar cin hanci a fadin kasar, zargin da a baya ake yiwa jami'an 'yan sanda.


📷 Premium Times

Post a Comment

Previous Post Next Post