Hukumar kula da harkokin man fetur ta NMDPRA ta yi gargaɗi ga gidajen mai da dillan man kan siyar da man fetur ga ƴan bunburutu.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafin X bayan ganawa da masu gidajen mai a birnin tarayya Abuja, hukumar ta ce ci gaba da siyar da man ga ƴan bunburutu zai kai ga dakatar da lasisin masu gidajen man.
Hukumar tayi bayanin cewa dole ne gidajen mai su dakata da siyar da man ta haramtattun hanyoyi, inda ta kara da cewa ƙin yin biyayya ga umarnin zai kai ga dakatar da siyar da man ga gidajen man.
"Hukumar NMDPRA ta fara yaƙi da siyar da mai ta haramtacciyar hanya , a jarkoki. Ana shawartar gidajen mai da su guji siyar da man ga yan bunburutu. Ƙin yin biyayya ga hakan zai kai ga dakatar da lasisin su".
NairaMetrics