Wasu mazauna jihar Kaduna sun koka kan yadda basa iya samar da abinci sau uku a rana ga iyalansu sakamakon matsin tattalin arziki da ake fuskanta da tsadar kayan abinci.
Wasu daga cikin mazauna garin da suka zanta da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, sun bayyana cewa yanke ciyar da iyalan nasu sau 3 a rana, yana da nasaba da matsin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar nan.
Wata matar aure mai suna Fatima Idris, ta ce mijinta ya umarce ta da ta dinga yin girki sau biyu a rana, wato karin kumallon safe da kuma abincin dare.
"Mijina albashi yake dauka duk wata na kasa da Naira dubun100; shekaru da suka gabata yana siyan shinkafa da wake da taliya ga ahalinsa. Amma yanzu ba zai iya haka ba.
"Shi yasa ya bukace ni nayi hakuri nayi amfani da dan abinda aka samu. Mu dinga yi ci sau 2 ni da yara a rana; a yanzu ma bama iya baiwa baki abinci", inji ta.
Anasa bangaren, Muhammad Bello yayi bayanin cewa ya fara azumin kwanaki 2 don neman lada da kuma rage kashe kudi na siyan abinci.
Yayi bayanin cewa yana shan ruwa da dabino idan yazo bude baki da kuma abinci.
Wani mazaunin jihar mai suna Adamu Mairiga, ya ce yana fafutukar samar da abinci sau uku ga iyalansa ta hanyar hakura da wasu bukatun nasa.
" Za su abinci, amma bana siyan nama ko kifi saboda wadannan sun yi tsada, ba zan iya siyan su ba. Sai dai ina iya siyan kwai sau 1 a wata.
"Yanayin da muke ciki a kasar nan, mazajen aure na cikin wani hali; daga biyan kudin makaranta zuwa abinci da kudin hanya, kawai muna rayuwa ne da Rahmar Ubangiji", inji shi.