Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi shugaban ƙasar, Bola Tinubu da 'neman mayar da Najeriya mallakin kansa'.
Atiku, ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 ya yi iƙirarin cewa Tinubu yana jinginar da makoman matasan Najeriya ga kansa da iyalinsa da kuma abokansa na kusa.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaÉ—a labarai, Paul Ibe ya fitar a jiya Laraba, inda ya bayyana damuwar sa kan cewa ko bayan Tinubu ya bar mulki, "zai yi wahala a warware abubuwan da ya kafa tare da kuma magance waÉ—annan matsalolin."
Atiku ya yi zargin cewa Tinubu na saƙala harkokin kasuwancinsa cikin harkokin gwamnati a Legas, tare da cewar irin hakan ne ke faruwa a yanzu a matakin tarayya.
Atiku ya ce a sanarwar "na yi matuƙar mamaki da gano cewa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya sanya ayyukansa na sayar da kayayyaki a ƙarƙashin kulawar OVH, wani kamfanin da Oando ke MALLAKIN kashi 49 cikin ɗari."
"Oando fa yana ƙarkashin jagorancin Wale Tinubu ne, ƙanen Shugaban Tinubu." in ji sanarwar.
Atiku ya bayyana baÆ™in cikinsa kan yadda a cewarsa "wasu kamfanoni da ke da kusanci da Tinubu Ssuka dabaibaye harkokin kamfanin NNPCL ba bisa ka’ida ba."
A wani sakon da ya wallafa a shafin sa na X a ranar Litinin, Atiku ya soki gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur wanda shi ne tushen halin da Æ´an Najeriya ke ciki
Tags:
LABARAI