Zaɓen ƙananan hukumomi: Dan takarar kansila na AAC ya kada na jam’iyya mai mulki PDP a Bauchi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar adawa ta AAC, Yunusa Muhammad a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Kansila a mazaɓar Papa a zaɓen ƙananan hukumomi da ya gudana a jihar.

Da ya ke bayyana sakamakon zaben a yau Asabar a cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta Darazo, baturen zaɓen, Muhammad Abdullahi Abubakar ya ce ɗan takarar jam’iyyar AAC ya samu kuri’u 1, 156, inda ya doke abokin karawarsa na PDP, Ashiru Mohammed wanda ya samu kuri’u 1, 053.

Sai ɗan takarar jam’iyyar APC, Idris Mohammed da ya na uku da kuri’u 290.

“Ni Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayina na baturen zabe na mazabar Papa a zaben da ya gudana a ranar 17 ga watan Agusta na 2024. Cewa Yunusa Muhammad na AAC ya cika ka’idar da doka ta tanada nake ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe”, inji shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post