Nijeriya da kasar China sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama a yayin ziyarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ga shugaba Xi Jinping a birnin Beijing, ciki har da ta makamashin nukiliya.
Yarjejeniyar, wacce aka sanya wa hannu a kai ta hada da samar da hanyoyi da makamashin ƙare-dangi na nukiliya da musayar bayanai kan kafafen yada labarai.
Nairametrics ta rawaito cewa an sanya hannun ne a gaban shugabannin kasashen biyu a jiya Talata.
Jaridar ta rawaito cewa hakan na zuwa ne, a yayin da shugaba Tinubu ke halartar taron kasar China da kasashen Afrika wanda zai gudana daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba na 2024.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar.
“A yayin ganawar, shugabannin biyu sun shaida sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan bangarori da dama”, inji sanarwar.
Acewar sa, yarjejeniyar zata karfafa alaka tsakanin Nijeriya da China.