Jam'iyyar NNPP ta ce APC ce ke daukar nauyin rikicin da ke faruwa a wasu jam'iyyun adawa a kasar nan domin ta ci gaba da rike mulki bayan shekarar 2027.
Ajuji Ahmed, Shugaban jam'iyyar NNPP na kasa ne ya bayyana hakan a taron kaddamar da yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam'iyyar a jihar Ondo, Olugbenga Edema, da aka yi a Akure, ranar Alhamis.
Ahmed ya zargi APC da katsalandan cikin harkokin cikin gida na jam'iyyun adawa ta hanyar haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin mambobinsu don raunana tsarin jam'iyyun da kwace iko.
A cewarsa, wannan lamari da APC ke yi na zuwa ne yayin da shugabannin jam'iyyun adawa ke shirin gudanar da "tattaunawar hade kai" don kawar da jam'iyya mai mulki gabanin babban zabe.
"APC na yin duk abin da za ta iya don lashe babban zaben 2027. Tabbas, akwai shaidu a ko'ina cewa suna katsalandan cikin sauran jam'iyyun. "Amma abin ya rage ga sauran jam'iyyun siyasa su kare mutuncinsu kuma su tabbatar sun kasance guda É—aya don kafa jam'iyyar adawa mai karfi da zata kawar da APC kafin da bayan zaben 2027," in ji shugaban NNPP.
Ya bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulki ta shirya mika mulki bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai jaddada cewa NNPP tana tare da jam'iyyun adawa domin kafa kawance gabanin zaben 2027.
"Saboda haka, kofar mu a bude take ta yadda idan za a samu hadin gwiwa tsakanin dukkan jam'iyyun siyasa don shiga zabe, muna shirye don hakan," in ji shugaban NNPP.
Tags:
LABARAI