Ba don gudunmuwar Tinubu ba, da Buhari bai zama shugaban ƙasa – Sunday Dare

 




Mai ba shugaban ƙasa shawara kan sadarwa da wayar da kan al'umma, Sunday Dare ya ce ba don gudunmuwar Tinubu ba, da Muhammadu Buhari bai samu nasarar lashe zaɓe ba a zaɓen 2015.


Dare ya bayyana hakan ne a shirin talabijin na Channels, inda ya ce, "idan ka kalla irin rawar da Tinubu ya taka wajen kafa jam'iyyar da Buhari ya yi takarar, zan iya cewa tabbas ba don gudunmuwar Tinubun ya bayar ba, da Muhammadu Buhari ba zai samu nasara a zaɓen ba," in ji shi.


Sunday Dare wanda tsohon minista ne a zamanin mulkin Buhari, ya ƙara da cewa sun yi aiki tuƙuru domin tabbatar da nasarar Buhari a zaɓen 2015 da 2019, inda ya ce, "mutane da dama sun bayar da gudunmuwa, kuma kowa da irin rawar da ya taka a zaɓen."


Ya ƙara da cewa, "yanzu zamanin Tinubu ne, kuma a shirye yake saboda yana da dukkan ƙwarewar da ake buƙata, kuma a shirye yake na yanke wasu matakan da shugabannin baya ba su ɗauka ba."


A ƙarshe ya ce akwai buƙatar a yaba wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa cire tallafin man fetur da sauran wasu tsare-tsaren da ya ɗauka domin inganta tattalin arzik

in ƙasar.


Post a Comment

Previous Post Next Post