📱 GOOGLE WALLET YA ISO NAJERIYA!
Shin ka taɓa jin labarin Google Wallet?
Google Wallet wani tsarin biyan kuɗi ne na zamani da kamfanin Google ya samar, wanda ke ba masu amfani damar haɗa katunan bankinsu da wayoyinsu domin gudanar da biyan kuɗi cikin sauƙi da tsaro.
Ta hanyar Google Wallet, za ka iya:
- Adana katin bankinka a wayarka.
- Biyan kuÉ—i a POS ta hanyar NFC (Contactless Payment).
- Adana wasu tikiti da katunan rangwame.
- Gudanar da wasu ayyukan biyan kuÉ—i na dijital.
🇳🇬 Me wannan ke nufi ga ‘yan Najeriya?
Zai ƙara buɗe wata hanya ta amfani da fasahar zamani wajen gudanar da harkokin kuɗi.
Sai dai ka sani, ba dukkan katunan banki ne ake tallafawa ba. Haka kuma, amfani da Contactless Payment yana buƙatar waya mai NFC.
Tambaya: Shin ka taɓa amfani da Google Wallet? Ko wannan ne karon farko da ka ji labarinsa?
Mu tattauna a comment section. 👇
Hassan Musa Himma Cybersecurity Awareness | Digital Safety


